Ingancin Tattalin Arziki

Ingancin Tattalin Arziki

By Rev. Fr. Luka Jatau

GABATARWA

Nasara ta wuce abin da mutum ya samo wa kansa, baban nasara shine abin da mutum ya zama a rayuwa. A rayuwan kowani Dan Adam, komi da komi na niman tattali: idan mutum yayi tattali Ransa, sai ya kai ga tsufansa da farin ciki. Wada kuma yayi tattali a Gidansa, zai nisance yunwa da cute-cute. Haka yake idan aka yi tattalin yara, sai su zama albarka ga kansu, iyayensu, da kuma jama’a duka. Mu sani da cewa baban rashi a rayuwan mutun ba mutuwan sa bane amma mutuwar basira da hangen nisa.

Baban damuwanmu a yau masamman a Vikariya ta Kontagora shine, mafi yawan mutane sun bada gaskiya cewa yadda rayuwasu ta zama masu, donle ne ta zama haka ga yayansu – ga yadda tunaninsu take; tunda mu bamu da ilimi, ilimi abin tsoro ne. Tunda bamu da martaba, ba mai yuwa bane yaramu suma su zama masu girma. Tunda an yi mana kami, babu wata hanyan aure sai kami. Tunda ba mu da aiki hanu, kada mu bar yaya mu su guje noma da muka gada. Irin wannan tunani ta gurguta kakaninmu, tana cizon iyayenmu yanzu, zata kuma sa yayanmu su zama bayi har abada.

To, tunda mun sami kanmu cikin wannan aloba, tambayoyin sune: ta yaya zamu inganta arzikin da muke da shi? Ta yaya zamu tsirar da yayamu daga zama bayi nan gaba? Ta yaya zamu bar addininmu ta karfafa a cikin rayuwanmu? Wannan sune dalilai da ya sa nake yin bayani akan “ingancin tattalin arzikin”.

Menene Tattalin Arzika

Arziki ta kunshi dukan abin da mutum ke dashi, wato kudade, dukiya, hikima, basira da kuma hangen nisa. Arziki shine, mutum ya tanadi isheshen abin biyan bukatun rayuwasa masu inganci. Dukan abubuwa masu inganci a rayuwan mutun sune arzikin sa.

Tattalin arziki kuma shine yadda mutum ke biye da abin da yake da shi domin yaduwanta da kuma daddewanta. Tattalin Arziki shine tsari domin inganta iyali, jari, ilimi, basira, fasaha da kuma kasuwanci. Wannan Tattalin Arziki shine niman karuwa akan abinda mutum zai iya yi da kuma abin da yeke da shi. A dungule kuma tattalin nan itace anfani da kowace dama da muka samu don bunkasa tsofofi da sabobin albarkatun da Allah ya bamu.

Hanyoyin bi don inganta arziki

Masu iya Magana sun ce abu mafi kyau a duniya shine ‘ilimi’, mafi muni kuma shine ‘jahilci’. Yawancin abubuwa da muke kira damuwa a rayuwanmu ba damuwa bane, amma rashin iyawa ne, domin ba wanda zai doki kudinsa ya ba mai gyaran Radio idan shima ya iya gyaranta. Saboda haka ga hanyoyin lura don inganta arzikimu.

Hangen Nisa: Hangin nisa ta kunshi sanin abin da ya kamata a yi yanzu domin nasarar gobe. Manomin da ke da hangin nisa zai saya maganin peshi a watan daya domin zuwa watan bakwai zasuyi tsada. Uban da ke da hangin nisa zai lura da cewa wata rana wurin noma zai kasa saboda haka dole ne a sa yara a sana’a da neman ilimi.

Illolin “Kami”: “Kami”, wato samo ma yaro ko yarinya na aure tun suna jarirai domin su yi girma tare. Wannan irin rayuwa ta gurgunta yara dayawa, tana kuma hana yara tunani mai zurfi domin cin gabansu. Iyaye dayawa sun bada gaskiya da cewa tunda an yi masu “Kami”, dolle ne su yi wa yayansu. Wannan irin tunanin ta tsufa amma har a yau muna rike da ita, in kuma mun cigaba da irin wannan tunani to mu sani haka ba hangen nisa bane.

Sanin Manufa Mai Yuwa: Lokacin da muke yara, mun sa kwazo ga makaran amma wasu abokananmu sun zatta mu wawayene. Lokacin da idanunsu suka bude, a wannan lokacin makaranta bai yuwa masu. Masu iya Magana sun ce “basira na rayuwa ba sanin lokacin samun nasara bane kawai amma sanin lokacin da nasara bai yuwa. Kowani mutum na da buri dayawa amma tambaya shine wannene zan iya aikatawa yanzu?

A wasu lokuta damuwamu shine bamu san yanda zamu ci nasara akan wasu burinmu sai in da taimakon wasu mutane, me zai hana mu basu daman yin haka? Yaro daga karkara zai iya zama babban malamin kimiya ko matuki Girgin sama, wanna abu ne mai yuwa amma mutane dayawa basu sani ba. Babban damuwanmu shine mun rena kanmu da kuma irin batsiran da Allah ya bamu. Dalilin yin haka kuma ya sa mun kasa cin gaba a duka alamuranmu. 

Tanadi Domin Gaba: Duk mai tafiya dole ne ya san inda zashi da kuma inda ya kamata ya bi. Duk rayuwan da babu tanadin gaba kamar Kadangare take, tayi kwai ta rufe da kasa ta wuce abinta. Wanda yake da karfin yin dakin haki, zai iya yin dakin kwanu amma sai da tattali. Ko wurin abinci ma mu kan nuna rashin tanadinmu, domin uwaye dayawa sukan yi albazaranci wurin dafa abinci – mu yi lura. 

A lokatai dayawa mukan gudu mu bar filayan domin niman kasa mai taushi na noma, kun sani da cewa idan filin noma ta gaji, bar filin na shekara daya sannan ku dawo mata. In kuma noma bai yuwa a fili, akwai ginegine nan gaba; kada ku gudu ku bar gonakinku ma wadansu. Kada ku sayar da gonakin domin baku noma akan su, gobe tafi yau yawa – fili ba don noma kadai ne ba. Fili kasa babbam Arzikine ama rashi hangen nisa ta sa mu cikin babam wahala.

A KARSHE

Tsarkaka Augustine yace idan za’a sami nasara a gaba, sai an lura da abubuwa biyu, Fushi – Fushi akan rashin azanci, rashin hangen nisa, rashin iya tattali da kuma rashin bada kai. Na biyu kuma shine karfin hali – karfin hali na canjin yadda muke duban rayuwa, canjin tunani domin gaba da kuma ba yara damman yanzu domin gaba. Kada mubar kaskancinmu yanzu ta sa mu kasa niman cingaba – Nasara takan faro a zuciya kafin ta fito fili. Yadda muke a yanzu cikin tunaninmu ne za mu zama gobe a cikin rayuwanmu. Allah ya taimake mu.

Author Image
Samie

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *